Shirin Haramin Imam Husain na Samar da Asibitin Khatimul Anbiya Don Masu ciwon zuciya yayi Nisa

Sashin Dabaru da tsara Ayyuka  na Haramin Husain ya sanar da ci gaba da  aikin Asibitin Khatimul Ambiya (AS) domin masu ciwon zuciya   Shugaban Bangaren Injiniyanci na Harami Muhammad Diya ya bayyana a wata hira da yayi da kafar yanar Gizon Hukuma cewa: Injiniyiyo da Kwararrun masana na Haramin Imam Husain mai Alfarma na ci gaba da aikin gina Asibitin Khatimul Ambiya (S) Don magance cututtukan Zuciya da jijiyoyin jini a cikin karbala, ya bayyana cewa yanzu yawan aiki yakai kaso 35%.       Yaci gaba da cewa aikin na daya daga cikin Muhimman Ayyukan da Hubbaren Imam Husain ke aiwatarwa da kuma kokarin samar da likitoci don biyan Bukatun Al'ummar Iraki, musamman wadanda ke fama ciwon Zuciya.      Ya kara da cewa girman aikin  yakai Murabba'in Mita 35,000 wanda zai  iya daukan Gadaje (141),  shi dai wannan Asibitin yana yankin Bahadaliyya ne dake cikin garin karbala mai tsarki, kuma ana gina aikin ne bisa tsarin cigaba na  kasa da kasa da kuma hanyar da suke wadanda suke bi wajen gina cibiyoyin kiwon lafiya.""      Ya cigaba da cewa aikin Asibitin ya kunshi manyan gine_gine guda biyu, daya daga cikin Su don taimakawa mutane ne dayan bangaren kuma an sadaukar da shi ne ga zaurika da kuma wuraren shakatawa,  Asibitin ya kunshi hawan Bene 11 ne sannan ko wanne Bene yakai Murabba'i mita (2,600) .     Abun lura dai shine ita hubbaren Imam Husain mai girma an nakalto ta hanyar  umarnin Wakilin Marji'iyya kuma limamin Haramin Shaik Abdul Mahdi  (Dz) cewa ita Harami tana ayyukan nan ne don tallafawa Iyalan Shahidai da Talakawa da sauran marasa galihu.

abubuwan da aka makala