Harin Bama -baman Amurka a filin Saukar jirgin saman Ƙasa da ƙasa na Karbala

Bayan harin bom da jiragen Amurka suka kai filin saukar jiragen sama na Ƙasa da ƙasa na Karbala da Haramin Imam Husain ke jagorantar ayyukan Wakilin Marji'iyya kuma Shugaban Haramin Sheikh Abdul Mahdi karbala'i Dz ya kai Ziyarar gani da ido Filin bayan shekara ɗaya da da kaddamar da harin. Da yake zantawa da kafofin sadarwa ta musamman Mataimakin Babban Sakataren Haramin kuma Wanda shine aka Jingina masa kulawa da Kamfanin Taiba wacce dake gudanar da ayyukan Ustaz Hasan Rashid Ubaiji yace ayyuka na tafiya a filin kuma tuni har an kammala samar da wasu ɓangarori duk da cewa dai ayyukan na tafiyar Hawainiya sakamakon cikas ɗin da aka fuskanta. Inda ya ƙara da cewa Kamfanin Taiba wacce ke gudanar da ayyukan ƙarƙashin inuwar Haramin Imam Husain ba zata taɓa kariya ba har sai ta cimma burin ta na ganin samun Nasarar abinda ta sa gaba. Ya kara da cewa Filin Saukar jiragen na Karbala zai taimaka wajen saukakawa masu Zuwa Ziyarorin wuraren Addini musamman Ziyarar Imam Husain da kuma Samar da ayyukan yi ga mutane. Idan ba'a manta ba dai a watan uku na shekarar da ta gabata ne Ataba Husainiyyah ta sanar harin bom da jiragen Amurka suka kai filin saukar jiragen na Karbala inda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutum ɗaya da kuma raunana wasu tare lalata da yawa daga ayyukan da aka gabatar.

abubuwan da aka makala